Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin Masu Saurare kan zaɓen Ghana

Informações:

Synopsis

Mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar jam’iyya mai mulki a Ghana, Mahamudu Bawumia ya amince da shan kaye a zaɓen ƙasar, inda ya taya tsohon shugaban ƙasa John Mahama murnar lashe zaɓen. Wannan ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a Asabar ɗin ƙarshen mako 7 ga watan Disamba, wanda rahotanni suka tabbatar da cewa ya gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.Shin ya ku ka kalli yadda zaɓen na Ghana ya gudana?Me za ku ce kan yadda Bawumia ya amince da shan kaye tun kafin a fitar da sakamakon zaɓen?Wane darasi ku ke ganin ƴan siyasa a yankunanku za su koya daga zaɓen Ghana?Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin