Tattaunawa Da Ra'ayin Masu Saurare

Ra'ayoyin masu sauraro kan kame mafi girma da EFCC ta yi a Najeriya

Informações:

Synopsis

A Najeriya, kwanan nan ne kotu ta karbe wani rukuni mai ƙunshe da gidaje 753 mallakin wani tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, nasara mafi girma da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ta taɓa samu a cikin sama da shekaru 21 da kafuwarta. Wannan shi ne maudu’in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a yau. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Oumaru Sani: