Bakonmu A Yau

Informações:

Synopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodes

  • Farfesa Abba Gambo kan matakan da gwamnatoci ke dauka a Najeriya game da noma

    16/05/2024 Duration: 03min

    Yanzu haka damina ta fara sauka a wasu sassan arewacin Najeriya, yayin da manoma ke shirin tinkarar aikin gona gadan gadan domin magance matsalar karancin abincin da kuma tsadar shi da aka fuskanta. Dangane da shirye shiryen noman, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Abba Gambo, mai bai wa gwamnonin Najeriya shawara a kan aikin noma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawarsu..........

  • Attahiru Bafarawa kan shirin ƴan adawa na tinkarar jam'iyya mai mulki a 2027

    15/05/2024 Duration: 03min

    A Najeriya, yanzu haka wasu daga cikin manyan ‘yan adawar ƙasar cikin su harda wadanda suka tsaya takarar zaɓen shekarar 2023 sun fara tintibar juna domin tsara yadda za su tinkari jam’iyya mai mulki a zaɓe mai zuwa. Rahotanni sun ce akwai yiwuwar kafa wata sabuwar jam’iyya domin kalubalantar gwamnati mai ci.Dangane da wannan yunkuri, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa. Kuna iya latsa alamar sauto domin sauraren hirar.

  • Farfesa Kailani Muhammed a kan batun satar danyen mai a Najeriya

    14/05/2024 Duration: 03min

    Hukumomin Najeriya sun ce sun kama jiragen ruwa 14 da ake satar danyan man fetur a Neja Delta tsakanin watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan Maris.Rundunar dake aikin samar da tsaro a Jihar Rivers tace wannan bai hada da kananan jirage 90 da kuma mutane 74 da ta kama ba, wadanda ke yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Kelaini Muhammed, masani a kan harkar gas da man fetur, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

  • Kwamandan MNJTF Janar Ibrahim Sallau kan nasarar su a yankin tafkin Chadi

    09/05/2024 Duration: 06min

    Rundunar hadin gwuiwa da ke yaƙi da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi da ake kira MNJTF ta sanar da kashe mayaka 299 a cikin watanni 10 da suka gabata da kuma samun wasu 273 da suka mika kansu cikin lumana. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Sallau Ali ya bayyana haka ga Babban Editan sashin Hausa Bashir Ibrahim Idris a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho bayan ya kwashe watanni 10 yana jagorancin rundunar mai cibiya a kasar Chadi.Ku latsa alamar sauti domin sauraren zantawar su.

  • Malam Issoufou Boubakar Magaji kan kudurin Benin na hana jiragen man Nijar safara

    08/05/2024 Duration: 03min

    Jamhuriyar Benin ta sanar da cewa ta dakatar da fitar da man da Nijar ke yi har sai ta dube iyakar da ta rufe. Danna alamar saurare don jin cikakkiyar tatttaunawar tare da Bashir Ibrahim Idris.

  • Dr Abdulhakeem Garba Funtua kan yadda Isra'ila ke shirin yin gaban kanta wajen kai hari Rafah

    07/05/2024 Duration: 03min

    Kungiyar tarayyar Turai da Amurka sun gargadi Isra'ila a shirin da take yi na kai hari Rafah, duk da cewa alamu sun nuna cewa kasar bata da shirin dakatar da kudurin nata. Danna alamar saurare don jin cikakkiyar tattaunawar tare da Bashir Ibrahim Idris

  • Farfesa Dicko Abdurrahmae kan zaben Chadi

    06/05/2024 Duration: 03min

    Yau Litinin aka bude rumfunan zabe a kasar Chadi, don zaben shugaban kasa da zai kafa sabuwar gwamnatin Chadi da ta kasance karkashin mulkin soji na tsahon shekaru 3. Kan wannan batu Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Dicko Abdurrahmane daga jamhuriyar Nijar, wanda ya yi bayani kan yadda yake kallon zaben.

  • Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya

    03/05/2024 Duration: 03min

    Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin. Sakamakon wannan biki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Umar Pate, shugaban Jami’ar Kashere, kuma shehun malami a bangaren horar da ‘yan jarida a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.

  • Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya

    02/05/2024 Duration: 03min

    Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.  Yanzu haka farashin litar man ya haura naira dubu biyu a wasu sassan Najeriyar, yayin da ake samun dogayen layuka a manyan birane irin su Lagos da Abuja da Kano.Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da farfesa Kelani Muhammed, kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron hirar da suka yi.

  • Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya

    01/05/2024 Duration: 03min

    Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu

  • Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira

    01/05/2024 Duration: 02min

    Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400. Sai dai a wannan makon Nairar ta sake samun tagomashi inda aka sayar dalar Amurka guda kan kasa da naira dubu 1,300.Ko me ya janyo rashin tsayuwar karfin Nairar, duk da irin matakan da bankin Najeriya ya ɗauka domin ba ta kariya? Tambayar kenan da muka yi Dr Ƙasim Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriyar.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da shi

  • Tattaunawa da Nuhu Abbayo Toro na TUC kan ranar ma'aikata a Najeriya

    01/05/2024 Duration: 03min

    Yau ake bikin ranar ma’aikata ta Duniya, wadda a bana ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarin matsalolin da a wasu sassa ko kasashe za iya cewa ruɓanyawa suka yi, musamman ma ƙalubalen matsin tattalin arziƙi. A Najeriya ‘Ranar Ma’aikatan ta bana ta zo wa ‘yan Ƙwadagon ƙasar ne cikin yanayin fuskantar tsadar rayuwa, kama daga tsadar kayan abinci, da man fetur har ma da wutar lantarki a baya bayan nan, duk da cewa ba ta samuwa.Kan haka ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro sakataren kungiyar kwadago ta Najeriya TUC, ga kuma yadda zantawarsu ta gudana game da wannan rana. 

  • Dr Kasim Kurfi kan yadda darajar nairar Najeriya ke kwan-gaba kwan-baya

    01/05/2024 Duration: 02min

    Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400. Sai dai a wannan makon Nairar ta sake samun tagomashi inda aka sayar dalar Amurka guda kan kasa da naira dubu 1,300.Ko me ya janyo rashin tsayuwar karfin Nairar, duk da irin matakan da bankin Najeriya ya ɗauka domin ba ta kariya? Tambayar kenan da muka yi Dr Ƙasim Kurfi, masanin tattalin arziƙi a Najeriyar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.

  • Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya

    29/04/2024 Duration: 03min

    Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500  a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.  Wannan kuwa na zuwa ne bayan watanni 11 da gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur da zummar bai wa kasuwa damar yin halinta. Kan haka Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Alhaji Bashir Dan Malam,shugaban Ƙungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas na Kasa a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar

  • Munyi mamakin yadda Amurka ta san bayanan sirrin tsaron mu - Raɗɗa

    26/04/2024 Duration: 05min

    Wasu gwamnonin arewacin Najeriya 10 da ke fuskantar matsalolin tsaro, sun kammala taron da suka je Amurka kan matsalar da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya. Gwamnonin sun ce sun samu bayanan sirrin tsaron jihohinsu a Amurkar fiye da yadda suke samu a Najariya.Ahmad Abba ya tattaunawa da gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda, wanda ya fara da yi masa bayani kan nasarar taron.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Bashir Dan-Malam kan karancin man fetur a sassan Najeriya

    25/04/2024 Duration: 03min

    Rahotanni daga sassan arewacin Najeriya na nuna cewar an fara samun karancin mai a gidajen mai, abinda ya sa wasu masu man suka kara farashin da suke sayar da kowacce lita. Bashir Ibrahim Idris ya tuntubi daya daga cikin shugabannin dillalan man a Najeriya, Alhaji Bashir Dan-Malam.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Alhaji Shehu Ashaka kan samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya

    24/04/2024 Duration: 03min

    Mahawara na ci gaba da zafi a Najeriya, dangane da yunkurin kirkiro ‘yan sandan jihohi domin taimakawa wajen inganta tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a. Yayin da wasu jama’a ciki harda gwamnonin jihohi da tsoffin shugabannin kasa ke cewa lokaci ya yi da za a samar da ‘yan sandan, wasu kuma ciki harda Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar na cewa har yanzu lokaci bai yi ba, saboda gwamnoni na iya amfani da su wajen biyan bukatun kan su. Dangane da wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Alhaji Shehu Ashaka, daya daga cikin dattawan Najeriya.Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana.......

  • Arewacin Najeriya aka fi kashe mutane a zangon farko na wannan shekarar - Rahoto

    23/04/2024 Duration: 03min

    Wani bincike da kamfanin Beacon Securities ya yi a Najeriya, ya ce a watanni 3 na farkon wannan shekarar an kashe mutane sama da 2,500, yayin da aka yi garkuwa da wasu sama da dubu 2. Rahotan ya ce kashi 80 na wannan aika aika ana samun sa ne a yankin Arewacin Najeriya. Dangane da haka Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Air Commodore Tijjani Baba Gamawa mai ritaya.  Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana......

  • Farfesa Mansur Isa Yelwa kan tsarin almajiranci a Najeriya

    22/04/2024 Duration: 03min

    A karshen makon da ya gabata ne zabtarewar kasa ta hallaka wasu almajirai guda 8 a Jihar Kebbi, matsalar da ta dada  tado da batun kula da almajiran da ke karatun Alkur'ani. Wasu na danganta matsalar da sakacin iyaye wajen rashin kula da 'ya'yan su ko kuma ciyar da su a makarantun allon. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Frafesa Mansur Isa Yelwa, daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci kuma masanin shari'a a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don jin cikakkiyar tattaunawarsu.......

  • Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike

    18/04/2024 Duration: 03min

    Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba. Kungiyar tace a cikin shekaru 10 da suka gabata, yankin ya gamu da mummanar ukuba, fiye da sauran sassan Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Dr Murtala Ahmad Rufai na Jami'ar Usman Danfodio, mawallafin 'I am a Bandit' kuma mai bincike a kan matsalar tsaron yankin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

page 1 from 2